Labarai

Kwanaki 4 bayan kashe mutane 12 mazauna wani kauye sun ce ‘yan ta’addan sun hana su kwashe gawarwakin domin binnewa a jihar Zamfara

Kwanaki 4 bayan kashe mutane 12 a Daraga, mazauna kauyen a jiya sun ce ‘yan ta’addan sun hana su kwashe gawarwakin domin binnewa.

Kauyen Daraga na yankin karamar hukumar Maru, daya daga cikin kananan hukumomin dake fama da ta’addanci sosai a jihar Zamfara.

A wani rahoto na musamman wanda BBC Hausa ta gabatar jiya da safe, mazauna kauyen sun ce baza su iya binne gawarwakin mutanensu ba, kasancewar har yanzu ‘yan bindigar suna kusa da kauyen.

Wani da ya nemi a sakaye sunansa, da ya zanta da BBC Hausa yace an kone gidansa gabadaya, kuma an kashe ubangidansa da dan’uwansa a shago.

A cewarsa, mutane sun fice daga kauyen zuwa wasu kauyuka daban-daban da suka hada da Dan Kurmi da Bena da Zargado, duka a jihar Zamfara, kuma wasu sun tafi kauyukan Wasagu da Unashi a jihar Kebbi.

Kakakin yansandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu, bai amsa kiran wayarsa ba, dangane da halin da ake ciki a Daraga.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: