Labarai

Kwankwaso ya kammala shirin bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 a karkashin jam’iyyar NNPP a mako mai zuwa

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya kammala shirin bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 a karkashin jam’iyyar NNPP a mako mai zuwa.

Da yake magana a wani taron manema labarai a jiya, Rabi’u Kwankwaso ya ce ya tuntubi mutane da dama kan aniyar ta sa, kuma ya samu martani mai kyau.

Tsohon gwamnan ya ce an samu karuwar masu goyon bayan jam’iyyar NNPP bisa la’akari da sakamakon da aka samu a aikin gangamin rajistar ‘ya’yan jam’iyyar da aka kammala kwanan nan.

Ya kara da cewa zaben 2023 zai kasance ne tsakanin masu son kawo sauyi a al’amuran Najeriya da kuma masu son abubuwa su cigaba da zama a yadda suke.

Rabi’u Kwankwaso ya kuma yi kira ga gwamnatoci da hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen magance tashe-tashen hankula, inda ya ce akwai bukatar gwamnati ta kara karfafa karfin jami’an tsaro wajen murkushe ‘yan ta’adda.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: