A karon farko tun watan Afrilu, yawan wadanda suka kamu da corona a Najeriya cikin rana guda yayi kasa da 100.

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta tabbatar da samun sabbin mutane 79 a jiyar Lahadi da dare, adadi mafi karanci a cikin kusan watanni biyar.

An samu sabbin mutanen a jihoshi 12 da babban birnin tarayya.

An kuma samu rahoton sabbin mutane 4 da cutar ta hallaka a jiyan, inda jumillar wadanda cutar ta kashe ya kai dubu 1 da 82.

Kazalika, da mutane 64 da suka warke kuma aka sallamesu a jiya, an samu rahoton karancin wadanda suka warke daga cutar a rana guda tun ranar 21 ga watan Mayu.

Daga cikin mutane dubu 56 da 256 da yanzu aka tabbatar sun kamu da cutar corona a jihoshi 36 da babban birnin tarayya, mutane dubu 44 da 152 sun warke.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: