

- Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta rufe kamfanonin ruwa guda 10 a jihar Ondo bisa rashin bin ka’idoji - July 4, 2022
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AA, Hamza Al-Mustapha, ya ce jam’iyyarsa ba za ta yi hadin gwiwa da mutanen da basu damu da makomar al’umma ba - July 4, 2022
- Yadda wani mutum ya kona matarsa bayan ya gama dukanta a jihar Ogun - July 4, 2022
Ministan Yada Labarai da Al’adu Alhaji Lai Muhammad, ya karyata labaran da wasu ke yadawa game da harbuwarsa da cutar Corona.
Ministan ya ce shi bai killace kansa ba, haka kuma bai karbi maganin cutar Corona ba, kamar yadda wasu hadiman shugaba Buhari suka harbu da cutar.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Ministan Mista Segun Adeyemi, ya fitar, ya ce Lai Muhammad, bai kamu da cutar Corona ba, haka kuma bai killace kan sa ba kamar yadda ake yadawa.
Sanarwa ta ce Ministan ya halarci zaman Majalisar Zartarwa a ranakun Laraba, Alhamis da kuma rantsar da Karamin Ministan Ayyuka da Gidaje ranar Juma’a.
Mista Adeyemi, ya ce yana mamakin yadda za’a ce Ministan da yake dauke da cutar Corona zai halarci tarukan da aka gudanar a ranakun.
Kazalika, Kakakin Ministan, ya ce Lai Muhammad, ya na cikin Kwamatin shugaban Kasa kan Yaki da Cutar Corona, saboda haka matukar yana dauke da cutar dole zai fadawa Jama’a.