Ma’aikatan Gwamnati Sun Gudanar Da Sallar Addu’a Domin Rashin Biyan Su Albashi A Jihar Zamfara

0 71

Wasu ma’aikatan gwamnati a jihar Zamfara sun gudanar da sallar addu’a domin rashin biyansu albashi da gwamnatin jihar ta yi.
Sun dai yi sallahr ne da safiyar jiya asabat da misalin karfe 10 na Safiya a filin idi dake Gusau babban birnin jihar.
Ma’aikatan sunce an biya su albashi na karshe a watan junairun wannan shekara, kuma sun kasance cikin mawuyacin hali tsawon lokacin da aka kwashe ba tare da albashin ba.
Duk kokarin jin tabakin gwamnatin jihar abin yaci tura, yayin da layin wayar kwamashinan yada labarai na jihar Ibrahim Dosara baya tafiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: