Ma’aikatar Lafiya ta ce amfani da ƙwarewar matasa na da muhimmanci wajen rage matsalar zazzabin cizon sauro

0 64

Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya tare da masana a ɓangaren masana’antar harhada magunguna sun bayyana cewa, amfani da ƙwarewar matasa na da matuƙar muhimmanci wajen rage ɗimbin matsalar zazzabin cizon sauro da ke addabar Najeriya.

Sun bayyana haka ne jiya a birnin Abuja, yayin ƙaddamar da gasar “Geneith Health Competition”, wani shiri da kamfanin Geneith Pharmaceuticals Ltd ya kaddamar tare da haɗin gwiwar CEOAFRICA domin yaƙi da cutar malaria a ƙasar.

Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, wanda Daraktan Lafiya ta Jama’a a ma’aikatar, Dakta Godwin Ntadom ya wakilta, ya ce Najeriya na ci gaba da fuskantar mummunar barazanar zazzabin cizon sauro duk da cewa wasu ƙasashe sun riga sun kawar da cutar baki ɗaya.

Shugaban Kamfanin Geneith Pharmaceuticals Ltd, Emmanuel Umenwa, ya bayyana cewa a shekarar 2023, an samu mutane 299 daga cikin kowane 1,000 da suka kamu da malaria a Najeriya, kuma hakan abin tsoro ne da ya isa a sanya dokar ta baci a sha’anin yaƙi da malaria cikin gaggawa.

Leave a Reply