Mai Martaba Sarkin Dutseya shawarci rundunar ‘yan sanda ta kasa da da ta tabbatar da tsaro mai inganci

0 84

Mai Martaba Sarkin Dutse, Dakta Nuhu Muhammadu Sanusi ya shawarci rundunar ‘yan sanda ta kasa da ta kara horas da jami’anta domin samun kwarin gwiwar dakile kalubalen tsaro a kasar nan.

Sarkin ya bada wannan shawarar ne lokacin da babban sufetan ‘yan sanda na kasa, Usman Alkali Baba ya kai masa ziyarar ban girma a fadarsa.

Dakta Nuhu Muhammadu Sanusi ya bayyana gamsuwa dangane da kwazon babban sufetan ‘yan sandan wajen ganin an kawo karshen ayyukan ‘yan fashin daji da sauran laifuka a kasar nan.

Mai martaba sarkin ya baiwa babban sufetan ‘yan sandan tabbacin samun hadin kai da goyon bayan sarakuna a kokarin da yake yi na tabbatar da bin doka da oda a kasar nan.

Tunda farko a nasa jawabin babban sufetan ‘yan sandan Usman Alkali Baba ya shedawa mai martaba sarkin cewa yaje fadarsa ne domin neman goyon baya da shawarwarinsa.

Yace sarakuna suna da muhimmiyar rawar da zasu taka wajen samun zaman lafiya da tsaro a kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: