Mai martaba Sarkin Kano ya yi kira ga mahukunta da su dauki matakin rigakafin cututtuka irinsu cutar kwalara

0 68

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi kira ga mahukunta da su dauki matakin rigakafin cututtuka irinsu cutar kwalara, maimakon mayar da hankali kan maganinta tunda cutar ta zamto wacce ke barkewa kowace shekara.

Sarkin ya yi wannan kiran ne a lokacin hira da manema labarai, wanda Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya shirya a fadarsa da ke birnin Kano.

Sarkin ya jaddada bukatar mutane su guji yin bahaya a sarari tare da rungumar tsaftar jik, a matsayin matakan dakile barazanar cutar.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su sami rigakafin corona da sauran rigakafin da suka dace kasancewar lokacin sanyi na gabatowa.

Ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki da abin ya shafa da su tabbatar da yin rijistar haihuwa a jihar, tare da rokon kafafen yada labarai da su kara himma wajen wayar da kan jama’a kan abubuwan da suka shafi kiwon lafiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: