Mai Martaba Sarkin Ringim, Dakta Sayyadi Muhmoud ya umarci Hakimai na masarautarsa da su tabbatar da dorewar shirin hana bahaya a bainar jama’a a gundumominsu.

Dakta Sayyadi Mahmoud ya bada wannan umarni ne lokacin da wakilan kwamatin hana bahaya a bainar jama’a na jihar Jigawa suka kai masa ziyarar bangirma a fadarsa.

Sarkin wanda ya samu wakilcin Galadiman Ringim, Alhaji Aliyu Muhammad, ya ce addinin Musulunci ma ya haramta tsuguno a bainar jama’a, inda ya yi fatan cewar dokar hana bahaya a fili da gwamnatin jihar Jigawa ta yi, ba za’a mai da ita siyasa ba domin baiwa sarakuna damar bada tasu gudummawar na tabbatar da ganin dokar tana aiki.

Alhaji Sayyadi Mahmoud ya kuma bayyana bukatar dake akwai na daukar ma’aikatan duba gari da kuma kara samar da bandakuna, musamman a kasuwanni da tashoshin mota da kuma makarantun tsangaya.

Tun farko a nasa jawabin shugaban Karamar Hukumar Ringim wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Mustapha Yunusa `Yan Dutse, ya bada tabbacin cewa majalissun kananan hukumomin masarautar za suyi duk abin da ya wajaba wajen samun nasarar dorewar shirin a yankunansu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: