Gwamnan jihar yobe mai mala buni ya bayyana cewa makomar jam’iyyar APC ta ta’allaka ne ga matasan kasar nan

Buni ya wanda shine shugaban kwamitin rikon kwarya na ja’iyyar ya bayyana hakan ne a wurin wani taron matasan jam’iyyar na kasa da aka gudanar a jiya litinin a babban birnin tarayya Abuja.

A cewarsa wannan taron shine na farko da aka fara gudanarwa a tarihin jama’iyyar, ya zo ne adaidai lokacin da ake shirin farfadowa, da kawo sauye sauye a cikin jam’iyyar.

Buni ya kara da cewa a karkashin jagorancin sa, yayi kokarin dawo da martabar jam’iyyar,da sake hada kan yayan jami’iyyar da aka batawa, tare da tabbatar da cewa suna iya bakin kokarin su wajan sanya matasa a mukamai daban daban a jagorancin jam’iyyar.

Tare da bada tabbacin cewa matasa a fadin kasar nan suna bada gagarumar gudunmawa wajan cigaban jam’iyyar.

Daga karshe ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa irin goyan bayan da yake bayarwa wajan cigaban jam’iyyar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: