Majalisar ƙaramar hukumar Dutse ta hana ma’aikatan da basu da katin shedar allurar rigakafin cutar Korona shiga Sakateriya

0 102

Majalisar Karamar Hukumar Dutse ta hana ma’aikatan da basu da katin shedar allurar rigakafin cutar corona shiga Sakatariyar Karamar Hukumar.

Shugaban karamar hukumar Bala Usman Chamo ne ya bayyana hakan a lokacin dayake kaddamar da gangamin yaki da cutar covid-19 a sakatariyar karamar hukumar dake birnin Dutse.


Manajan Hukumar lafiya matakin farko na Karamar Hukumar, Malam Abdulhamid Ibrahim Kudai wanda kuma shi ne Jagoran tawagar jami’an gudanar da allurar rigakafin cutar, ya ce shugaban Karamar Hukumar, Malam Bala Usman Chamo ne ya bada wannan umarni.


Shugaban Karamar Hukumar ya ce duk wanda bai gabatar da katin shedar yi masa rigakafin cutar ba, ba za a bari ya shiga Sakatariyar ba.


Malam Abdulhamid Ibrahim Kudai ya kara da cewa duk ma’aikacin da ba a yiwa rigakafin ba , za a yi masa nan take kafin shiga Sakatariyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: