Majalisar Dattawa Baza Ta Iya Hana Shirin Rushe Ofisoshin Hukumomin Sufurin Jirgin Sama Ba A Filin Jirgin Saman Legas

0 51

A wani labarin kuma, ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, yace majalisar dattawa baza ta iya hana shirin rushe ofisoshin hukumomin sufurin jirgin sama ba a filin jirgin saman Murtala Mohammed dake Lagos.

Hadi Sirika, wanda ya yiwa manema labaran fadar shugaban kasa jawabi bayan zaman majalisar zartarwa ta tarayya, na mayar da martani dangane da umarnin majalisar dattawa na cewa a dakatar da aikin rushe ofisoshin hukumar kula da filayen jiragen sama na kasa da hukumar kula da sararin saman Najeriya da kuma hukumar kula da sufurin jiragen sama, har sai an samu rahoton binken ayyuka da kwamitin majalisar na sufurin jiragen sama ke gudanarwa.

Yace hukuncin na majalisar shawara ce kawai, inda yayi nuni da cewa za a gudanar da rusau din ne domin kawata filin jirgin saman da kuma hana tashin gobara a guraren na wucin gadi.

Ya nanata jajircewar gwamnati na samar da kamfanin sufurin jiragen sama na kasa, inda ya bayyana kwarin gwiwar cewa gwamnati mai zuwa za ta cigaba da aikin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: