Majalisar Dattawa ta amince da ƙudirin kuɗaɗe na bana wanda shugaba Buhari ya aika mata makonni 2 baya

0 92

Majalisar Dattawa a jiya ta amince da kudirin kudade na bana, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika mata makonni 2 baya.

Amincewa da kudirin cikin mako biyu ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitocin hadin gwiwa na kudade da kwamitin kwastan da na haraji da na kasuwanci da zuba jari.

Shugaban kwamitin hadin gwiwar, Solomon Adeola, a jawabin da ya gabatar, yace kudirin na neman tallafawa aiwatar da kasafin kudin badi ta hanyar samar da dokokin da ake bukata na haraji da kwastan da sauransu.

A cewar dan majalisar, jumillar dokoki 12 aka yiwa gyara a karkashin kudirin kudaden dake dauke da sassa 39.

Ya kara da cewa kudirin na nufin kawo gyara a harkokin kudade da gyara dokokin haraji kamar yadda suke a sauran kasashen da suka cigaba, da fito da harajin ababen more rayuwa da na kasuwannin hannun jari tare da tallafawa kananan ‘yan kasuwa da nufin inganta hanyoyin samun kudaden shiga ga gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: