Labarai

Majalisar dattawa ta amince da wani kudiri na neman gyara dokar hana ta’addanci ta 2013, tare da kuma haramta biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane a Najeriya

Majalisar dattawa ta amince da wani kudiri na neman gyara dokar hana ta’addanci ta 2013, tare da kuma haramta biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane a Najeriya.

Zartar da dokar hana ta’addanci ta 2013 da aka gyara a 2022, ya biyo bayan nazarin rahoton da kwamitin shari’a, ‘yancin dan adam da al’amuran shari’a suka yi.

Shugaban kwamitin, Sanata Opeyemi Bamidele na jam’iyyar APC daga jihar Ekiti ne ya gabatar da rahoton kafin a amice da shi.

A nasa jawabin Opeyemi Bamidele, ya ce kudirin dokar ya tanadi haramta biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan ta’adda domin a sako duk wani wanda aka sace.

A cewar dan majalisar, kudirin dokar an samar da shi ne da nufin dakile karuwar yawaitar satar mutane domin neman kudin fansa a Najeriya, wanda ke yaduwa a fadin kasarnan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: