Majalisar dattawa ta amince wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ciwo bashin fiye da dala biliyan 16

0 75

Majalisar dattawa ta amince wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ciwo bashin dala biliyan 16.2.

Majalisar ta amince da buƙatar ciyo bashin ne da Shugaba Buhari ya gabatar mata a watan Mayu, kuma bashin yana cikin tsarin ciwo bashi na 2018 zuwa 2020 na gwamnatin tarayya.

Majalisar ta amince da buƙatar ne a zamanta na jiya Laraba.

Gwamnatin tarayya zata ciwo basukan daga bankin duniya da kuma asusun bada basuka na kasar China, wanda nijeriya zatayi amfani da kudaden wajan habbaka masana’antu da kuma karasa wasu ayyuka.

Amincewar ta biyo bayan la’akarin da majalisar ta yi ne da rahoton kwamitinta a kan basussukan cikin gida da na waje.

Shugaban kwamitin majalissar na kasa mai kula da basuka Senator Clifford Ordia ya tabbatar da amincewar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: