Kwamatin Hukumar Kidaya na Majalisar Dattawa a jiya ya bayyana cewa kimanin Naira Biliyan 190 ne aka ware domin gudanar da Kidayar Jama’a shekarar 2022 mai zuwa.

Shugaban Kwamatin Sanata Sahabi Alhaji Ya’u shine ya bayyana hakan ga manema labarai bayan ya kare kasafin kudin hukumar na shekarar 2022, a gaban Kwamatin Kasafi na Majalisar.

A cewarsa, aikin wanda za’a gudanar a shekarar 2022, zai lashe Naira Biliyan 190, kuma suna jiran amincewar shugaban Kasa kafin fara aikin.

Da ake bayyana yadda aikin ya ci karo da shirye-shiryen zaben shekarar 2023, sanatan ya ce suna tunanin shine lokacin da ya dace da gudanar da aikin.

Kazalika, ya ce hukumar ta kallama dukkan shirye-shiryenta, kuma shugaban Buhari ya amince da a gudanar da kidayar cikin shekarar 2022.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: