Majalisar Dattawan kasar nan ta amince da nadin mutum biyar a matsayin Kwamishinonin Zaɓe na Jihohi a hukumar INEC, bayan nazarin rahoton kwamitinta kan harkokin zaɓe a yau Laraba.
Wadanda aka tabbatar da su sun haɗa da Umar Yusuf Garba daga jihar Kano, Sa’ad Umar Idris daga jihar Bauchi, Chukwuemeka Ibeziako daga jihar Anambra, Umar Mukhtar daga jihar Borno da kuma Dr. Johnson Alalibo daga jihar Bayelsa.
Sanata Sharafadeen Alli wanda ya gabatar da rahoton ya ce dukkansu sun cika dukkan sharuddan doka da ƙwarewa da ake buƙata domin rike mukamin.
Shugaban Majalisa, Sanata Godswill Akpabio ya taya su murna tare da bukatar su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da adalci domin inganta tsarin dimokuraɗiyya a ƙasar nan.