Majalisar Dinkin Duniya ta ce yanzu haka ‘yan gudun hijira miliyan daya ne suka tsere daga Ukraine zuwa kasashe makwabta

0 30

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yanzu haka ‘yan gudun hijira miliyan daya ne suka tsere daga Ukraine zuwa kasashe makwabta.

Tserewar dumbin ‘yan gudun hijirar na zuwa ne cikin kwanaki bakwai kacal bayan mamayar kasar da Rasha da ta fara a makon jiya Alhamis.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ta shafin Twitter, kwamishinan hukumar ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya, Filippo Grandi, ya roki a tsagaita wuta domin a samar da agajin jin kai na ceton rai ga miliyoyin mutanen da suka rage a kasar.

Hukumar ta yi hasashen rikicin zai raba mutane kimanin miliyan 12 da mahallansu cikin bukatar agaji.

Leave a Reply

%d bloggers like this: