Majalisar Dinkin Duniya tace yaƙin Ukraine ya jefa mutane sama da miliyan 70 cikin talauci a fadin duniya

0 166

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa hauhawar farashin abinci da man fetur sakamakon yakin Ukraine ya tilastawa mutane miliyan saba’in da daya a kasashe masu tasowa cikin talauci tun watan Maris.

Hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce hauhawar farashin kayayyaki na yin illa ga marasa ƙarfi, tare da yin mummunar illa musamman a kasashen Balkan da tsakiyar Asiya da kuma yankin kudu da hamadar Sahara.

Ta yi gargadin cewa, kara yawan kudin ruwa a manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a matsayin wata hanyar dakile hauhawar farashin kayayyaki na fuskantar barazanar kara ta’azzara matsalar ga kasashe masu tasowa da ake bi dimbin basussuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: