Majalisar dokokin Jigawa na shirin gabatar da dokar adalci da haɗin kai domin samar da daidaito ga al’ummar jihar
Majalisar dokoki ta jihar Jigawa na shirin gabatar da kudurin dokar bambanci da adalci da haɗin kai, domin samar da daidaito da cigaba ga al’ummar jihar.
Kakakin majalisar, Rt. Hon. Haruna Aliyu Dangyatin, ya bayyana hakan yayin da yake karɓar shugabar cibiyar kare haƙƙin haihuwa ta CRR, Dr. Abiola Akinyode Afolabi, a ziyarar da ta kai masa don neman goyon baya.
Dangyatin ya jaddada cewa majalisar za ta yi duba mai zurfi kan kudurin don tabbatar da dacewarsa da tsarin addini da al’adu na jihar, tare da tabbatar da cewa dokar za ta amfanar da rayuwar tattalin arziki da zamantakewar jama’a.
Dr. Afolabi ta bayyana cewa kudurin an tsara shi tare da masana daga jami’o’i, kuma ta bukaci Jigawa ta aiwatar da dokar dakile mutuwar mata masu ciki, da ta ce tuni jihar ta dabbaka wasu dokoki irin.