Majalisar dokokin jihar Jigawa ta dakatar da wasu shuwagabannin ƙananan hukumomin 4

0 407

A dai nan jahar Jigawa majalisar dokokin jahar ce ta dakatar da wasu shuwagabannin ƙananan hukumomin jahar guda huɗu, bisa zarginsu da  rashin tafiyar da harkokin kuɗaɗen ƙananan hukumomin su yadda ya kamata, yayinda majalisar ta maida guda ukun data dakatar a kwanakin baya.

Kazalika majalisar ta tsige mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar da bulaliyar majalisar daga kan muƙaman su bisa zarginsu da hannu a yunƙurin tsige kakakin majalisar da baiyi nasara ba a kwanannan  tare da maye gurbin su da wasu nan take.

Daga Dutse wakilin mu Zulkiflu Abdullah Dagu ya aiko mana da ƙarin bayani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: