Majalisar dokokin jihar Jigawa ta yi gyara a dokar oditoci ta jiha da kuma kara wasu sassa a cikin dokar

0 67

Majalisar dokokin jihar Jigawa ta yi gyara a dokar oditoci ta jiha da kuma kara wasu sassa a cikin dokar.

Gyaran dokar da kuma kara wasu sassa ya biyo bayan wasikar da Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya aikewa majalisar wadda ke bukatar yin gyaran.

A lokacin zaman shugaban majalisar, Alhaji Idris Garba Jahun ya ce gyaran dokar zai samar da karin iko ga babban mai binciken kudi na jiha da na kananan hukumomi kan batun da ya shafi kasafin kudi da kashe kudi da kuma bunkasa kwazon ma’aikata.

Shugaban kwamatin majalisar mai lura da asusun gwamnati wanda shi ne wakilin mazabar Kazaure, Barista Bala Hamza Gada ya ce an kara sashi na 20 da na 26, yayin da aka yi gyara a sashi na 7 da na 8 da kuma na 10 da nufin tabbatar da ingantuwar ayyuka a matakin jiha da kananan hukumomi.

Wakilin mazabar Kanya Babba Alhaji Usman Haladu ne ya gabatar da kudirin amincewa da gyaran dokar, inda ya samu goyan bayan wakilin mazabar Miga, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: