Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta zartar da ƙudurin kasafin kuɗin baɗi na Naira biliyan 177 da miliyan 795

0 145

Majalisar Dokokin Jihar Jigawa a jiya ta zartar da kudurin kasafin kudin badi na Naira biliyan 177 da miliyan 795 da dubu 588, wanda ya zama doka.

An rattaba hannu kan kasafin kudin jim kadan bayan kwamitin kasafin kudi ya gabatar da rahotonsa.

Shugaban kwamitin kudi da kasafin kudi na majalisar, Suleiman Musa Kadira ne ya mika rahoton.

A ranar Laraba 10 ga watan Nuwamba ne Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya gabatar da kudirin kasafin kudi na shekarar mai zuwa ga majalisar dokokin jihar.

Ya ce an ware kudaden albashi da Alawus-alawus na ma’aikata sama da naira biliyan 53, sai kudaden gudanar da aikin gwamnati sama da naira biliyan 33 yayin da kudaden manyan ayyuka suka haura naira biliyan 90.

Kakakin majalisar Idris Garba Kareka ya yabawa kwamitin kudi da kasafin kudi na majalisar bisa kokarin da suka yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: