Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Amince da Kudirin Dokar da Zai Bai Wa Gwamnatin Jihar Damar Kafa Rundunar ’Yan Sandan Jiha.
Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini Dala, ya ce matakin ya biyo bayan amincewa da gyare-gyaren da Majalisar Wakilai ta yi domin sauƙaƙa kafa ’yan sandan jiha a faɗin ƙasar.
Kazalika, majalisar ta amince da buƙatar Gwamna Abba Kabir Yusuf na rage kasafin kuɗin jihar na shekarar 2026 sakamakon sauyin da aka samu dangane da ƙiyasin da aka yi wa alƙaluman kuɗaɗen shiga.
Da farko, jihar ta amince da kasafin kuɗin Naira tiriliyan 1.477 na shekarar 2026, sai dai majalisar ta ce raguwar kuɗaɗen da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya, sakamakon sauye-sauyen dokokin haraji, ta tilasta sake duba kasafin.
Sabon kasafin ya ragu daga Naira tiriliyan 1.477 zuwa tiriliyan 1.222, domin daidaita kashe kuɗaɗen gwamnati da yanayin alƙaluman kuɗaɗen shigar jihar suke ciki.