Majalisar karamar hukumar Birnin Kudu a nan jihar Jigawa ta amince da daurin shekaru biyu ga duk wanda aka kama da yanke bishiya ba tare da izinin gwamnati ba.

Shugaban karamar hukumar Magaji Yusuf ne ya bayyana haka a jiya a wani taro da aka gudanar a garin Birnin Kudu.

Ya ce majalisar ta amince da dokar ne a wani bangare na kokarin da take yi, na rage yawan saren itatuwa domin hana gurbatar muhalli.

Ya bayyana cewa a karkashin dokar duk wanda aka kama yana yanke bishiya ba tare da hukumomin da abin ya shafa ba, zai fuskanci fushin doka.

Magaji Yusuf ya kara da cewa majalisar ta kafa wani kwakkwaran kwamati da zai yi aiki tare da jami’an tsaron dazuzzukan, da nufin kama duk wani mai saran bishiya ba tare da izinin gwamnati ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: