

- Yadda yan IPOB suka kashe ‘yan Arewa 10 ciki har da mace mai juna biyu da ‘ya’yanta 4 da wasu mutane 6 a jihar Anambra - May 24, 2022
- Sama da mutane 30 ne aka ruwaito sun bace a jihar Borno bayan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai musu hari - May 24, 2022
- Tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, ya karbi tikitin takarar Sanatan Gombe ta Arewa domin tsayawa takara a jam’iyyar PDP a 2023 - May 24, 2022
Majalisar Karamar Hukumar Hadejia ta kaddamar da wani kwamiti mai wakilai 17 kan cigaban tsarin tsaftar muhalli.
Da yake kaddamar da kwamitin, shugaban majalisar, Alhaji Abdulkadir Bala T. O ya ce ana sa ran kwamitin zai yi aiki bisa kiyayewa da sharuddan da aka gindaya masa.
Jami’in yada labarai na karamar hukumar Muhammad Garba Talaki ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya aikawa kafafen yada labarai ciki har da Sawaba.
Sanarwar ta ce an umurci kwamitin da ya gabatar da rahotonsa cikin makonni biyu.
Mambobin kwamitin sun hada da Alhaji Adamu Abdullahi a matsayin Shugaba da Muhammad Abdullahi a matsayin sakatare, yayin da hakimai uku, Babban Limami da jami’in yada labarai da sauransu, suka zama mambobin kwamitin.