Majalisar Karamar Hukumar Hadejia tasha alwashin hukunta duk mai Babur da ta kama da laifin tukin ganganci

0 182

Majalisar Karamar Hukumar Hadejia tasha Alwashin daukar Matakan doka domin hukunta duk mai Babur Mai Kafa da ta kama da laifin tukin ganganci.

Shugaban Karamar Hukumar Alhaji Abdulkadir Bala Umar T.O, shine ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin Jagororin Kungiyar a Ofishin sa.

A cewarsa, karamar hukumar ta samu rahoton yadda masu baburan suke janyo hadari da kuma asarar rayuka.

Shugaban ya ce karamar hukumar bazata sassautawa duk mutumin da ta kama da laifin tukin ganganci ba a yankin.

Alhaji Abdulkadir Bala Umar T.O ya bukaci Jagororin kungiyar su fadawa sauran mambobin su, suyi rijista da karamar hukumar domin samun Izini.

Kazalika, ya ce karamar hukumar tana tunanin bullo da hanyoyin da zama tsugunnar da Masu Baburan.

Tun farko a jawabinsa, Shugaban Kungiyar Malam Ali Abdullahi, ya ce sun kawo ziyara ofishin shugaban ne domin gabatar da kansu, tare da neman hadin kai karamar hukumar.

Haka kuma ya ce Mambobin kungiyar zasu rika biyan kudaden shiga ga karamar hukumar, tare da daukar alkawarin bin dokokin da karamar hukumar ta shinfida.

Leave a Reply

%d bloggers like this: