Majalisar magabata ta kasa ta amince da watan Afrilu na shekarar 2023 don gudanar da kidayar jama’a da hukumar kidaya ta kasa za ta gudanar

0 41

majalisar magabata ta kasa a jiya ta amince da watan Afrilu na shekarar 2023 don gudanar da kidayar jama’a da hukumar kidaya ta kasa za ta gudanar.

Darakta-Janar na Hukumar Kidaya ta Kasa, Nasir Isa-Kwarra ne, ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa bayan kammala zaman majalisar magabatan wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Isa-Kwarra ya kuma ce hukumar za ta gudanar da kidayar gwaji daga watan Yuni na shekarar da muke ciki, bayan jam’iyyun siyasa sun kammala shirye-shiryensu kafin zaben gama-gari.

Darakta Janar na hukumar, ya tunatar da cewa an gudanar da aikin kidayar jama’a na karshe a shekarar 2006, yana mai cewa hukumar za ta yi amfani da fasahar zamani domin aikin na gaba.

Ya ce ana amfani da bayanan kidayar domin tsarawa, inda yayi nuni da cewa bayanan da ake amfani da su a halin yanzu na hasashe ne kawai kuma lokacinsu ya wuce.

Leave a Reply

%d bloggers like this: