Majalisar Wakilai ta amince da a sake ciyo basukan kuɗaɗe daga ƙasashen waje fiye da Dala biliyan 5 da miliyan 803

0 168

Majalisar Wakilai a jiya ta amince da ciyo basukan kudade daga kasashen waje wadanda suka kai jumillar dala biliyan 5 da miliyan 803 da dubu 364 da 553, kimanin naira tiriliyan 2 da biliyan 379 da miliyan 205 da dubu 365 da 998 da kobo 40, kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nema.

Majalisar ta kuma amince da karbo tallafi na musamman na dala miliyan 10 ga gwamnatin tarayya, biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin kula da tallafi, bashi da lamuni dangane da jadawalin ciyo basukan kasashen waje na 3 na shekarar 2018 zuwa 2020.

Shugaban kwamitin, Ahmed Safana Dayyabu ne ya gabatar da rahoton.

Za a ciyo basukan daga bankin duniya da gamayyar kamfanoni Jamus da bankin cigaban musulunci da bankin Exim na China da bankin gwamnatin China da asusun cigaban aikin gona na kasa da kasa.

Ana kuma sa ran samun tallafin na musmaman daga gamayyar kamfanoni Jamus.

Leave a Reply

%d bloggers like this: