Majalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Domin Bincika Zargin Karkatar da Kudi Naira 20Bn

0 70

A jiya Alhamis ne majalisar wakilai ta kafa wani kwamitin wucin gadi da zai binciki zargin karkatar da Kudi Naira biliyan 20 da wasu ma’aikatan kamfanin man fetur na kasa suka yi.
Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da Hafiz Ibrahim Kawu dan majalissa daga jihar Kano ya gabatar.
An ruwaito cewa ma’aikatan kamfanin na NNPC, sun karkatar da sama da Naira biliyan 20 a matsayin kudin tuntuba da aka biya wa mashawartan sa.
Ya ce a yayin da gwamnatin tarayya ke yin iya kokarinta na yaki da cin hanci da rashawa da kuma yin amfani da albarkatun kasa wajen bunkasa ababen more rayuwa na kasa, ma’aikatan hukumar na karkatar da kudade.
Ya ce idan har majalisar ba ta yi wani abu ba don duba wannan al’adar da ba ta dace ba, hakan zai shafi arzikin kasa tare da hana gwamnatocin jihohi samun kudaden shiga.

Leave a Reply

%d bloggers like this: