Majalisar wakilai ta kafa wani kwamiti da zai binciki tsadar kayayyakin abinci da kayayyakin masarufi

0 83

Majalisar wakilai ta kafa wani kwamiti na musamman da zai binciki tsadar kayayyakin abinci da kayayyakin masarufi a fadin kasarnan.

Kwamitin wanda aka kafa a jiya zai kasance karkashin jagorancin mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar, Peter Akpatason daga jihar Edo.

Kafa kwamitin ya biyo bayan amincewa da bukatar hakan da dan majalisa Ibrahim Isiaka daga jihar Ogun, ya gabatar.

Babban aikin kwamitin shi ne kaddamar da sauraron jin ra’ayin jama’a tare da dukkan masu ruwa da tsaki a kasar nan da kuma gudanar da bincike kan musabbabin hauhawar tsadar rayuwa.

Da yake gabatar da kudirin, Ibrahim Isiaka ya ce farashin kayayyakin abinci sun yi tashin gwauron zabi da kashi 100 a sassa da dama na kasarnan, cikin shekara guda da ta gabata.

Ya dora alhakin tsadar kan manufofin kudi da sauran manufofin kasafin kudi na gwamnati, gami da rufe iyakokin kasarnan hade da matakan dakile cutar corona da kuma rashin tsaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: