Majalisar Wakilai ta kuduri aniyar bincikar yadda aka gudanar da ayyuka na musamman na ma’aikata dubu 774 na gwamnatin tarayya.

Majalisar ta umarci kwamitocin ta na kula da ma’aikata da na rabon kudi, rage radadin talauci da sauran kwamitocin da abin ya shafa da su binciki yadda aka aiwatar da shirin.

Hakan yazo ne sakamakon kudirin da Muhammad Gudaji Kazaure ya gabatar a jiya yayin zaman majalisar.

Shirin ya janyo cece-kuce tsakanin karamin ministan kwadago da samar da ayyukan yi Festus Keyamo da ‘yan majalisar wakilai a bara.

Kimanin Naira Biliyan 52 aka ware domin shirin ayyukan na musamman a kasafin kudin shekarar 2020.

An tsara shirin ne, da nufin daukar mutane dubu 774 aiki, kusan dubu daya daga dukkan kananan hukumomi 774 da ke kasarnan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: