A yau ne Majalisar Wakilan Najeriya za ta fara tsefe rahoton kwamitin sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin dokar haraji.
Kakakin Majalisar, Hon. Tajudeen Abbas ne ya bayyana haka a zaman majalisar na ranar Laraba.
Hon Tajudeen ya ce majalisar za ta ɗauki tsawon wunin yau, Alhamis tana nazari da muhawara kan sassan ƙudirin dokar daban-daban.
Kakakin majalisar ya kuma yi kira ga duka mambobin majalisar su halarci zaman domin bayar da tasu gundonmawa kan rahoton kwamitin sauraron ra’ayin jama’ar.
Tuni dai kwamitin sauraron ra’ayin jama’ar – ƙarƙashin jagorancin shugaban kwamitin kuɗi na majalisar, Hon James Abiodun Faleke – ya kammala sauraron jin ra’ayin jama’a inda ya miƙa rahoton nasa a gaban majalisar a ranar Talata
A watan Oktoban bara ne shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya gabatar da ƙudurori huɗu da suka shafi haraji a gaban majalisun dokokin ƙasar, domin amincewa da su.