Majalisar Zartarwa ta Jigawa ta amince da fitar da naira miliyan 279 domin tallafawa Ƙungiyar Direbobi
Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da fitar da naira miliyan dari biyu da saba’in da tara domin tallafawa Ƙungiyar Direbobi ta Najeriya wato NURTW reshen jihar a matsayin wani shiri na ƙarfafa tattalin arzikinsu.
Kwamishinan Muhalli, Dr. Nura Ibrahim, ya bayyana hakan ga manema labarai bayan zaman majalisar da Gwamna Umar Namadi ya jagoranta a gidan gwamnati.
Za dai a yi amfani da kudin ne wajen siyo motoci iri daban-daban da za a raba wa mambobin kungiyar 36. Haka kuma, an ƙara fitar da naira miliyan dari huɗu da talatin da ɗaya don tallafawa ƙananan masana’antu 58 a jihar, tare da wasu ƙarin aikace-aikace 17 da suka haura naira miliyan goma sha tara da ke jiran amincewa.