Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da kashe Miliyan 836 domin siyo Na’urar taimakawa Numfashi

0 63

Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince ta kashe Naira Miliyan 836 domin siyo Na’urar taimakawa Numfashi ta Oxygen a cigaba da yaki da cutar Corona a kasar nan.

Da yake yiwa manema labaran fadar shugaban Kasa Jawabi, bayan kammala zaman Majalisar Ministan Yada Labarai Alhaji Lai Muhammad, ya ce amincewar ta biyo bayan bukatar hakan da Ministan Lafiya Dr Osagie Ehanire ya gabatarwa Majalisar.

A cewarsa, Ministan Lafiyar ya kuma gabatar da kubutar a sake gyara wasu Na’urorin Oxygen 38 domin raba su a kasar nan.

Ministan ya ce Majalisar ta kuma amince da sake fadada tare da yashe Madatsar Ruwa ta Bawai wanda suke nomar Rani da ita akan Naira Miliyan 302.8

Haka kuma ya kara da cewa aikin Madatsar ta Bawai an fara ne tun cikin shekara 2005 kuma akayi watsin dashi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: