Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da kudi naira miliyan 449 da dubu 900 domin tuntubar masana akan inganta tsarin tafiyar da filayen jiragen sama 17 a Najeriya.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Mallam Garba Shehu ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa jiya bayan kammala taron majalisar.
Garba Shehu ya lissafta filayen jiragen saman da suka hada da na Murtala Muhammed na kasa da kasa dake Lagos, da na Nnamdi Azikiwe na kasa da kasa da ke Abuja, da na filin jiragen saman kasa da kasa na Fatakwal da filin jiragen saman kasa da kasa na Mallam Aminu Kano dake Kano.
Sauran sun hada da filayen jiragen sama na Owerri, da Imo, da Benin, da Edo, da Enugu, da Maiduguri, da Yola, da Calabar, da Ilorin, da Sokoto, da Ibadan, da Jos, da Akure da kuma na Katsina.
Garba Shehu ya ce majalisar ta kuma amince da kudi naira biliyan 3 da miliyan 400 domin bayar da shawarwari daga kwararru bayan kammala kwangilar gina titin jirgin sama na biyu da kayan aikin titin a filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.