Majalisar zartarwar tarayya ta amince da sayen motoci 46 domin gudanar da aiki a hukumar yaki da fasa kwauri ta kasa, customs.

Karamin Ministan Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-tsaren kasa, Mista Clem Agba, ya shaidawa manema labaran fadar shugaban kasa bayan zaman ganawar majalisar ta internet wanda mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya jagoranta jiya a Abuja.

Ministan yace motocin zasu habaka karfin gudanar da ayyukan hukumar tare da inganta samar da kudaden shiga.

Yace zuwa watan Augustan 2021, hukumar customs ta samar da kudaden shiga masu yawa fiye da adadin da aka tsara.

Mai bawa shugaban kasa shawara akan kafafen yada labarai, Femi Adesina, shima ya yiwa manema labaran fadar shugaban kasa bayani dangane da sauran abubuwan da aka amince da su a zaman majalisar.

Adesina yace an samu amincewar gina ofishin shugabannin jami’a da dakin taro mai daukar mutane dubu 1 a Jami’ar Abuja akan kudi naira miliyan dubu 2 da miliyan 300.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: