Majalisar Zartaswa Ta Tarayya Ta Amince Da Sabon Daftarin Bunkasa Masana’antar Kera Motoci Ta Kasar

0 157

Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da sabon daftarin bunkasa masana’antar kera motoci ta kasa na shekarar 2023.

Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Niyi Adebayo ne ya gabatar da takardar kudirin daftarin a taron majalisar zartarwa ta tarayya a jiya wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

An fara taron ne bayan addu’o’in da Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Digital Isah Ali Pantami da takwaransa na ayyuka na musamman Sanata George Akume suka jagoranta.

Wadanda suka halarci taron majalisar sun hada da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan.

Haka kuma, babban daraktan hukumar kera motoci ta kasa Jelani Aliyu da sauran hadiman shugaban kasa sun halarci taron.

Majalisar kula da kera motoci ta kasa ce ta samar da daftarin domin tabbatar da dorawa akan nasarorin da aka samu kawo yanzu a masana’antar kera motoci ta kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: