Majalissar Dinkin Duniya ta bukaci da a samar da kimanin dala miliyan 600 domin tallafawa kasar Afghanistan

0 232

Majalissar dinkin duniya ta bukaci da asamar da kimanin dala milyan 600 domin tallafawa kasar Afghanistan, tare da cewa kasar tana bukatar taimakon jin kai.

Bukatar taimakon kasashen duniyar ya biyo bayan zaman da majalissar ta shirya a Geneva, bayan kungiyar Taliban ta kwace iko da kasar a watan da ya gabata.

Majalissar Dinkin duniyar ta bayyana cewa samar da tallafin dala milyan 606 zai tallafawa milyoyin mutane a kasar.

Da yake jawabi a wajan taron, sakatare janar na majalissar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya bukaci kasashen duniya da su taimakawa kasar Afghanistan wajen ceto tattalin arzikin ta da kuma taimakawa mata tare da wadanda ‘yancin su ke fuskantar barazana.

Sakataren yace a bayyane take, wannan gidauniyar da aka kaddamar ba wai ta kunshi abinda za’a baiwa kasar ba ne, harma da bashin da kasar ke bin kasashen duniya.

Daga cikin Dala miliyan 606 da ake saran tarawa domin aikin jinkai a Afghanistan, akwai kudaden da za’a karkata wajen ciyar da jama’ar dake fama ad yunwa da kuma taimakawa marasa lafiya.

Sakataren yace Majalisar zata bada Dala miliyan 20 daga cikin asusun agajin gaggawan ta na Turai domin gudanar da aikin jinkai a Afghanistan, amma bukatar da ake da ita a kasar ta zarce abinda Majalisar ke da shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: