Majalissar karamar hukumar Guri tace tana da kudi fiye da naira miliyan 4 a asusun tara kudaden shiga na yankin.

Shugaban Alhaji Musa Shu’aibu Muhammad Guri ya bayyana hakan ta cikin shirin radio Jigawa.

Yace sakamakon bullo da sabbin dabarun hanyoyin samun kudaden shiga, a yanzu haka karamar hukumar ta ninka kudaden shigar sau 5.

Alhaji Musa Shuaibu Muhammad Guri yace karamar hukumar ta gyara fanfunan tuka tuka 415 yayin da karamar hukumar ta mayar da gidajen ruwa na police station dana garin Gabargal zuwa masu amfani da hasken rana domin inganta harkar bada ruwansha a yankin.

Haka kuma gwamnatin jiha ta mayar da gidan na garin Guri zuwa mai amfani da hasken rana akan kudi naira miliyan 19.

Shugaban karamar Hukumar ta Guri yakara da cewar Karamar hukumar ta gina fadar Hakimin Guri kan kudi fiye da naira miliyan arbain da aikin gina masalaci a garin Musari kan kudi naira miliyan 19 da gyaran masalacin juma’a na Adiyani kan kudi miliyan 12 da aikin sanya naurar bada ruwansha mai amfani da hasken rana a garin Margadu kan kudi bakwai da kuma aikin gina cibiyar lafiya a Dagana kan kudi miliyan 17.
06/12/2021     

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: