Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a jiya ya gudanar da zaman ganawa tare da shugabannin hukumomin ilimi bisa zargin karin kudin makaranta a wasu makarantun gaba da sakandire.

Shugaban hukumar kula da jami’o’i, Abubakar Rasheed, da shugaban hukumar kula da kwalejojin ilimi, Paulinus Okwelle, sun halarci zaman ganawar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa Bilkisu Ahmad, wacce ta wakilci hukumar kula da makarantun fasaha, ta halarci zaman ganawar.

Ahmad Lawan a jawabinsa na maraba yace ya kira zaman ne domin samun cikakken bayanai akan matsalar wacce ka iya haifar da rikici a bangaren ilimi idan ba a maganceta cikin gaggawa ba.

Da yake mayar da martani a madadin shugabannin hukumomin, Abubakar Rasheed ya yabawa Ahmad Lawan bisa sanya baki a lokacin da ya dace.

Yace hukumomin zasu tuntubi makarantun gaba da sakandire dangane da matsalar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: