Majalissar Tattalin Arziƙin Ƙasa Ya Kafa Kwamitin Sanya Ido

0 166

Majalissar tattalin arzikin kasa ya kafa kwamitti domin duba yawan adadin kundin da asusin ajiya na kamfanin mai na kasa ke ciki da sauran batutuwa da suka shafi kamfanin.

Gwamnan jihar Adamawa Ahmed Fintiri ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala taron, wanda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo ya jagoranta a fadar gwamantin Najeriya.

Yan kwamittin sun hada da gwamnonin jihohin Edo, Jigawa da kuma Ebonyi.

Ya ce sakataren ma’aikatar kudi ta kasa ya bayyana musu yawan kudin da asusun ya ajiye a ranar 19 ga watan Yuni sama da dala milyan 144.

Leave a Reply

%d bloggers like this: