Malaman Najeriya za su fara cin gajiyar sabon tsarin albashin da Shugaba Buhari ya yi alkawari

0 110

Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, ya ce malaman Najeriya za su fara cin gajiyar sabon tsarin albashin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawari daga watan Janairun badi.

Nwajiuba ya bayyana hakan jiya a Abuja a wani taron karawa juna sani da ma’aikatar ilimi ta shirya.

Taron karawa juna sani wani bangare ne na shirye-shiryen bikin ranar Malaman Makaranta ta Duniya ta bana mai zuwa.

Ministan, ya samu wakilcin babban sakataren ma’aikatar, Sonny Echono.

Ya kuma bayyana cewa ana shirin kammala aiki a kan sauran matakan walwala da jin dadi, wadanda shugaban kasar ya yi alkawari a bikin Ranar Malaman Makaranta Duniya ta bana. Ya jaddada cewa sauran matakan walwala da jin dadi da zasu karawa malaman makarantar Kwarin gwiwa, sun hada da Alawus-alawus, da gidaje, da bayar da horo, da kuma kara shekarun aiki daga 35 zuwa 40.

Leave a Reply

%d bloggers like this: