Masarautar Daura ta nada Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi a matsayin dan Amanan Daura

0 46

Masarautar daura ta nada ministan Sufuri Rotimi Amaechi a matsayin dan Amanar Daura.

Bikin nadin wanda ya gudana da safiyar yau a jihar katsina ya samu halartar tawagar da shugaban kasa Muhammadu buhari ya aika.

A wata sanarwa da shugaban ya fitar a ranar Juma’a ya yaba wa Amaechi da kuma hamshakin dan kasuwa Nasiru Haladu Danu da suka samu rawanin sarautar a Daura.

Ana nadawa Alhaji Danu rawani a matsayin Tafida Babba na Daura.

Buhari ya bayyana Amaechi da “Dan Amana” (wanda aka amince da shi) a matsayin sadaukar da kai ga dangantakar da ke tsakanin sa da yankin duk da irin bambance-banbancen al’adu da ake dashi a kasar nan. Shugaba Buhari ya tura tawaga guda uku da suka hada da ministan albarkatun ruwa, Engr Sulaiman Adamu, da takwaran sa na sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika, da kuma babban mataimaki na musamman kafofin yada labarai da yada labarai, Garba Shehu, da za su wakilce shi a wajen taron.

Leave a Reply

%d bloggers like this: