Masu sarautun gargajiya a Jihar Jigawa sun sha alwashin bada hadin kai da goyan baya ga Hukumar Kidaya ta Kasa

0 59

Masu Sarautun Gargajiya a Jihar Jigawa, sun sha Alwashin bada hadin kai da Goyan Baya ga Hukumar Kidaya ta Kasa domin tabbatar da cewa ta gudanar da aikin Kidayar Jama’a mai cike da gaskiya a shekarar 2023.

Mai Martaba Sarkin Dutse, Dakta Nuhu Muhammadu Sanusi, shine ya bayyana hakan a lokacin da Kwamishinan Hukumar Kidaya ta Kasa a Jihar Jigawa, Alhaji Garba AG Zakar ya kai masa ziyara fadar sa.

Sarkin na Dutse, bada tabbacin cigaba da bada dukkanin gudummar da ta kamata, musamman fadakar da matasa muhimmancin shiga shafin sadarwa na hukumar, domin daukansu aiki na wucin gadi.

Sarkin ya ce Kidayar Jama’a na daga cikin abubuwan da suke ciyar da kasa gaba.

Haka kuma ya ce tuni Masautar ta kafa kwamati domin cigaba da bibiyar aikin domin samun nasarar da ake bukata.

Tun farko a Jawabinsa, Kwamishinan Hukumar Kidaya ta Kasa, Alhaji Garba AG Zakar, ya ce sun kawo masa ziyara fadar sa ne domin fadar da shi aikin da suke gudanarwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: