Masu zanga-zanga sun fito a biranen Najeriya domin kokawa kan halin da ƙasar ke ciki a yau Alhamis

0 129

A birnin tarayya Abuja, daruruwan mutane sun fito zanga-zangar lumana a ranar Dimokiraɗiyya domin nuna fushinsu kan matsin rayuwa da tsaro mara tabbas a faɗin ƙasar.

Ko da yake jami’an tsaro sun bazu a manyan hanyoyi da wuraren taro kamar ginin majalisar dokoki, masu zanga-zangar sun mamaye unguwar Apo suna ɗaga kwalaye da rera taken adawa da halin da ƙasa ke ciki.

Wannan zanga-zangar na zuwa ne a daidai lokacin da damuwa ke ƙaruwa dangane da rashin ci gaban tattalin arziki da ƙaruwar tashe-tashen hankula da kuma jin cewa dimokiraɗiyyar ta kasa kawo sauyi a rayuwar talakawa.

Har zuwa tsakiyar rana, zanga-zangar ta kasance cikin lumana, sai dai hukumomi na cikin shiri don kaucewa duk wani rikici.

Leave a Reply