Kimanin jarirai 25 ne aka Haifa a sansanin yan gudun hijra da ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu na kauyen Karnaya dake karamar hakumar Dutse a nan jihar jigawa.

Daya daga cikin masu rua da tsaki a yankin na Karnaya Falalu Ado ya bayyana haka ga manema labarai a sansanin.

Kauyen Karnaya dai na daya daga cikin garuruwan da ambaliyar ruwan ta fi shafa a jihar jigawa wanda ya raba dubban yan kauyen da gidajensu.

Ado yace mata 25 suka haihu a sansanin tun bayan tasowarsu daga matsuguninsu na asali makonni biyu da suka gabata.

Malama Rukayya Sani daya ce daga cikin matan masu shayarwa a yanzu haka bayan ta haifi jariri namiji wanda aka sanyawa sunan mai martaba sarkin Gumel Ahmad Muhammad Sani, domin nuna godiyar su ga sarkin bisa kokarinsa na jibintar lamuransu.

Babban sakataren hakumar lafiya matakin farko na jihar jigawa Dr. Kabir Ibrahim yace gwamnatin jiha ta bayar da motoci 3 ga sansanin domin ayyukan gaggawa ga mutanen.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: