Labarai

Mataimakin Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi, shine ya lashe zaben fidda gwani na dan takarar gwamna a jam’iyyar APC

Mataimakin Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi, ya lashe zaben fidda gwani na dan takarar gwamna a jam’iyyar APC.

Da ake sanar da sakamakon zaben wanda aka gudanar a filin taro na Mallam Aminu Kano dake birnin Dutse, an ayyana Umar Namadi a matsayin wanda ya samu nasara da kuri’u dubu 1 da 220, sai Muhammad Sabo Nakudu yazo na biyu da kuri’u 106.

Sanata Ibrahim Hassan Hadejia yazo na uku da kuri’u 58, sai Faruku Adamu Aliyu wanda ya samu kuri’u 15, sai kuma Sani Hussaini Garin Gabas mai kuri’u 5.

Umar Namadi babban akawu kuma ya kafa kamfaninsa na manyan akawu a Kano a shekarar 1993.

A matsayin wanda ya fara rike shugaban sashen asusun kudaden kamfanin Dangote, Umar Namadi shine ya assasa ginshikin samar da bayanan kudaden kamfanin na Dangote a kowane wata.

Tsohon kwamishinan kudi na jihar Jigawa ya kuma kasance wakili a kwamitin tantancewa da tabbatar da kwangiloli da tantance ma’aikata.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: