Mataimakin gwamnan jihar Jigawa ya kaddamar da cibiyar fasahar sadarwa ta zamani wanda hukumar inganta rayuwar mazauna kan iyakoki ta kasa ta samar a garin Gumel

0 72

Shugaban Kwamitin shata kan iyakoki na jihar Jigawa kuma mataimakin gwamnan jiha Mallam Umar Namadi ya kaddamar da cibiyar fasahar sadarwa ta zamani wanda hukumar inganta rayuwar mazauna kan iyakoki ta kasa ta samar a garin Gumel.

A jawabinsa wajen kaddamarwar Mallam Umar Namadi ya bayyana samar da cibiyar da hukumar ta yi a matsayin abin alfahari ga jama’ar Gumel da kuma jihar nan baki daya.

Umar Namadi wanda ya samu wakilcin sakataren kwamitin, Alhaji Muhammad Garba Malammadori, ya bada tabbacin yin cikakken amfani da cibiyar ta hanyar da ta dace

A nasa jawabin sakataren zartarwa na hukumar, Junaid Abdullahi yace hukumar ta gudanar da ayyuka a bangarorin aikin gona da kiwon lafiya da kuma ilimi.

Sakataren, wanda ya samu wakilcin Ibrahim Kwajafa, ya yabawa gwamnatin jiha bisa hadin kai da goyan bayan da take baiwa aiyukan hukumar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: