Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar, Abba Kyari ya garzaya wata babbar kotun tarayya domin neman belinsa

0 58

Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar Abba Kyari, ya garzaya wata babbar kotun tarayya a yau domin neman belinsa.

Abba Kyari da wadanda ake tuhumar su uku, ta bakin lauyansu, sun bukaci mai shari’a Emeka Nwite da ya bayar da belinsu saboda rayuwarsu a gidan gyaran hali na Kuje inda ake tsare da su na fuskantar barzana.

A ci gaba da sauraron karar, Onyechi Ikpeazu, lauya ga Abba Kyari tare da mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar Sunday Ubia, ya sanar da cewa an shigar da bukatar neman belin wadanda ake kara tare da gabatar da su a hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA.

Ya ce bukatar belin ta zama dole saboda yanayin aikin da wadanda ake tuhumar suka yi a aikinsu na ‘yan sandan.

Lauyan ya ce ana ci gaba da tsare wadanda ake tuhumar a waje daya tare da masu aikata laifuka a gidan gyaran da’a, wadanda ta hanyarsu aka samu nasarar cafke su.

Babban Lauyan ya ce rayukansu na cikin hadari, don haka ake bukatar belinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: